Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 17:25-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Amma lalle sai ya sha wuya iri iri tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ƙi shi.

26. Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka kuma zai faru a lokacin bayyanar Ɗan Mutum.

27. Ana ci, ana sha, ana aure, ana aurarwa, har ya zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi, Ruwan Tsufana kuma ya zo, ya hallaka su duka.

28. Haka ma aka yi a zamanin Lutu, ana ci, ana sha, ana saye, ana sayarwa, ana shuke-shuke da gine-gine,

29. amma a ranar da Lutu ya fita daga Saduma, aka zubo wuta da duwatsun wuta daga sama, aka hallaka su duka.

30. Haka kuma zai zama a ranar bayyanar Ɗan Mutum.

31. A ran nan fa wanda yake kan soro, kayansa kuma na cikin gida, kada ya sauko garin ɗaukarsu. Haka kuma wanda yake gona, kada ya juyo.

32. Ku tuna fa da matar Lutu.

33. Duk mai son adana ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa, adana shi ya yi.

34. Ina gaya muku, a wannan dare za a ga mutum biyu a gado ɗaya, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.

35. Za a ga mata biyu suna niƙa tare, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya. [

36. Za a ga mutum biyu a gona, a ɗau ɗaya, a bar ɗaya.]”

37. Sai suka amsa suka ce, “Ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, “A inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.”

Karanta cikakken babi Luk 17