Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 14:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wata ranar Asabar, ya shiga gidan wani shugaba Farisiyawa garin cin abinci, mutane kuwa suna haƙwansa.

2. Sai ga wani mai ciwon fara a gabansa.

3. Yesu ya amsa ya ce wa masanan Attaura da Farisiyawa, “Ya halatta a warkar ran Asabar ko kuwa?”

4. Sai suka yi shiru, Yesu kuwa ya riƙe shi, ya warkar da shi, ya kuma sallame shi.

5. Sa'an nan ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da jaki ko takarkari ya faɗa a rijiya ran Asabar, ba zai fitar da shi nan da nan ba?”

6. Sai suka kasa ba da amsar waɗannan abubuwa.

7. To, ganin yadda waɗanda aka gayyato sun zaɓi mazaunan alfarma, sai ya ba su misali ya ce,

8. “In an gayyace ka zuwa biki, kada ka zauna a mazaunin alfarma, kada ya zamana an gayyato wani wanda ya fi ka daraja,

9. wanda ya gayyato ku duka biyu kuma yă zo ya ce maka, ‘Ba mutumin nan wuri.’ Sa'an nan a kunyace ka koma mazauni mafi ƙasƙanci.

10. Amma in an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi ƙasƙanci, don in mai gayyar ya zo, sai ya ce maka, ‘Aboki, hawo nan mana.’ Za ka sami girma ke nan a gaban dukan waɗanda kuke zaune tare.

11. Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”

12. Ya kuma ce da mai gayyar, “In za ka kira mutum cin abinci ko biki, kada ka riƙa kiran abokanka kawai, ko 'yan'uwanka, ko danginka ko maƙwabtanka masu arziki, kada su ma su gayyace ka, su sāka maka.

13. Amma in za ka kira biki, sai ka gayyayo gajiyayyu, da musakai, da guragu, da makafi,

Karanta cikakken babi Luk 14