Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 11:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wata rana Yesu yana addu'a a wani wuri. Bayan da ya gama, sai wani a cikin almajiransa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka koya mana addu'a, kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa.”

2. Sai ya ce musu, “In kuna addu'a ku ce,‘Ya Uba, a kiyaye sunanka da tsarki,Mulkinka yă zo,

3. Ka ba mu abincin yau da na kullum.

4. Ka gafarta mana zunubanmu, gama mu ma muna gafarta wa duk wanda yake yi mana laifi.Kada ka kai mu wurin jaraba.’ ”

5. Ya kuma gaya musu, “Misali, idan waninku yana da amini, ya je wurinsa da tsakar dare ya ce masa, ‘Wāne, ranta mini gurasa uku mana,

6. ga shi, wani abokina matafiyi ya sauka a wurina yanzu, ba ni kuwa da abincin da zan ba shi,’

7. sa'an nan aminin ya amsa masa daga ciki ya ce, ‘Kada ka dame ni, ai, an kulle ƙofa, da ni da 'ya'yana duk mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka wani abu ba.’

8. Ina gaya muku, ko da yake ba zai tashi ya ba shi wani abu don yana amininsa ba, amma saboda nacinsa zai tashi ya ba shi ko nawa yake bukata.

Karanta cikakken babi Luk 11