Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 1:68-78 Littafi Mai Tsarki (HAU)

68. “Ubangiji Allahn Isra'ila,A gare shi ne lalle yabo yake tabbata,Domin ya kula, ya yi wa jama'a tasa fansa.

69. Ya ta da Mai Ceto mai iko dominmu,Daga zuriyar baransa Dawuda.

70. Yadda tuntuni ya faɗa ta bakunanAnnabawa nasa tsarkakan nan,

71. Yă cece mu daga abokan gābanmu,Har ma daga dukan maƙiyanmu.

72. Domin nuna jinƙai ne ga kakanninmu,Ya tuna da alkawarinsa mai tsarkin nan.

73. Shi ne rantsuwan nan wadda ya yi wa ubanmu Ibrahim,

74. Domin yana cetonmu daga abokan gābanmu,Mu bauta masa ba da jin tsoro ba,

75. Sai dai da tsarki da adalci a gabansa,Dukan iyakar kwanakin nan namu.

76. Kai kuma, ɗan yarona, za a ce da kai annabin Maɗaukaki,Gama za ka riga Ubangiji gaba,Domin ka shisshirya hanyoyinsa,

77. Kă sanar da ceto ga jama'a tasa,Wato ta samun gafarar zunubansu,

78. Saboda tsananin jinƙai na Allahnmu,Daga Sama hasken asubahi zai ɓullo mana,Daga can Sama ne fa zai keto mana,

Karanta cikakken babi Luk 1