Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 1:50-61 Littafi Mai Tsarki (HAU)

50. Daga zamanai ya zuwa wani zamani,Jinƙansa yana ga waɗanda suke tsoronsa.

51. Manyan ayyuka da ya yi,Masu girmankai, su da dabarbarunsu ya warwatsa.

52. Ya firfitar da sarakuna a sarauta,Ya ɗaukaka ƙasƙantattu.

53. Mayunwata ya ƙosar da abubuwan alheri,Mawadata kuwa ya sallame su hannu wofi.

54. Ya taimaka wa baransa Isra'ila,Domin yana tunawa da jinƙansa.

55. Ya cika faɗarsa ga kakanninmu,Ga Ibrahim da zuriyarsa, har abada.”

56. Maryamu kuma ta zauna tare da Alisabatu wajen wata uku, sa'an nan ta koma gida.

57. To, lokacin Alisabatu na haihuwa ya yi, ta kuwa haifi ɗa namiji.

58. Sai maƙwabta da 'yan'uwanta suka ji yadda Ubangiji ya ji ƙanta ƙwarai, har suka taya ta farin ciki.

59. Sai ya zamana a rana ta takwas suka zo yi wa ɗan yaron kaciya. A dā za su sa masa sunan ubansa, Zakariya,

60. amma uwa tasa ta ce, “A'a, Yahaya za a sa masa.”

61. Sai suka ce mata, “Ai kuwa, ba wani ɗan'uwanku mai suna haka.”

Karanta cikakken babi Luk 1