Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Luk 1:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Tun da yake mutane da yawa sun ɗauka su tsara labarin waɗannan al'amura da suka tabbata a cikinmu,

2. daidai yadda waɗanda suke shaidu tun farkon al'amari, masu hidimar Maganar, suka rattaba mana,

3. da yake kuma na bi diddigin kowane abu daidai tun farko, ni ma dai na ga ya kyautu in rubuta maka su bi da bi, ya mafifici Tiyofalas,

4. domin kă san ingancin maganar da aka sanar da kai baki da baki.

5. A zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar Abaija. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu.

6. Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.

7. Amma ba su da ɗa, don Alisabatu bakararriya ce, dukansu biyu kuma sun tsufa.

8. Ana nan, wata rana Zakariya na kan hidima tasa ta firist, a sa'ad da hidimar ta kewayo kan ƙungiyarsu,

9. bisa ga al'adar hidimar firistoci, sai kuri'a ta nuna shi ne mai shiga Haikalin Ubangiji, ya ƙona turare.

10. A lokacin ƙona turare kuwa duk taron jama'a suna waje, suna addu'a,

11. sai wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, yana tsaye a dama da bagadin ƙona turare.

Karanta cikakken babi Luk 1