Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Kol 4:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku iyayengiji kuma, ku riƙi bayinku da gaskiya da daidaita, da yake kun sani ku ma kuna da Ubangiji a Sama.

2. Ku lazamci yin addu'a, kuna zaune a faɗake a kanta sosai, tare da gode wa Allah,

3. mu ma ku yi mana addu'a Allah ya buɗe mana hanyar yin Maganarsa, mu sanar da asirin Almasihu, wanda saboda shi ne nake a ɗaure,

4. domin in bayyana shi sosai, kamar yadda ya kamata in faɗa.

5. Ku tafiyar da al'amuranku da hikima a cikin zamanku tare da marasa bi, kuna matuƙar amfani da lokaci.

6. A kullum maganarku ta zama mai ƙayatarwa, mai daɗin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.

7. Tikikus zai sanar da ku duk abin da nake ciki. Shi ƙaunataccen ɗan'uwa ne, amintaccen mai hidima, abokin bautarmu kuma a cikin Ubangiji.

8. Na aiko shi a gare ku musamman, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa muku zuciya.

9. Ga kuma Unisimas a nan tare da shi, amintaccen ɗan'uwa ƙaunatacce, wanda shi ma a cikinku yake. Su za su gaya muku duk abin da ya faru a nan.

10. Aristarkus, abokin ɗaurina, yana gaishe ku, haka kuma Markus, wanda kakansu ɗaya ne da Barnaba. Shi ne aka riga aka yi muku umarni a game da shi. In dai ya zo wurinku, ku karɓe shi.

Karanta cikakken babi Kol 4