Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Kol 3:17-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Kome kuke yi, a game da magana ko aikatawa, ku yi duka da sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta wurinsa.

18. Ku matan aure, ku bi mazanku yadda ya dace a cikin Ubangiji.

19. Ku maza, ku ƙaunaci matanku, kada kuma ku yi musu kaushin hali.

20. Ku 'ya'ya, ku yi wa iyayenku biyayya ta kowane hali, domin haka Ubangiji yake so.

21. Ku ubanni, kada ku ƙuntata wa 'ya'yanku, domin kada su karai.

22. Ku bayi, ku yi biyayya ga waɗanda suke iyayengijinku na duniya ta kowace hanya, ba da aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai da zuciya ɗaya, kuna tsoron Ubangiji.

23. Kome za ku yi, ku yi shi da himma kuna bauta wa Ubangiji ne, ba mutum ba,

24. da yake kun sani Ubangiji zai ba ku gādo sakamakonku. Ubangiji Almasihu fa kuke bauta wa!

25. Mai mugun aiki kuwa za a sāka masa da mugun aikin da ya yi, babu kuma tāra.

Karanta cikakken babi Kol 3