Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Kol 1:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Shi ya sa tun a ran da muka ji labarin, ba mu fāsa yi muku addu'a ba, muna roƙo a cika ku da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu,

10. domin ku yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, kuna faranta masa ta kowane fanni, kuna ba da amfani a kowane aiki nagari, kuna ƙaruwa da sanin Allah.

11. Allah yă dai ƙarfafa ku da matuƙar ƙarfi bisa ga ƙarfin ɗaukakarsa, domin ku jure matuƙa a game da haƙuri da farin ciki,

12. kuna gode wa Uba, wanda ya maishe mu mu isa samun rabo cikin gādon tsarkakan da suke a cikin haske.

13. Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa,

14. wanda ta gare shi ne muka sami fansa, wato, gafarar zunubanmu.

15. Shi ne surar Allah marar ganuwa, magāji ne tun ba a halicci kome ba,

Karanta cikakken babi Kol 1