Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Kol 1:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, tare da Timoti, ɗan'uwanmu,

2. zuwa ga tsarkaka da amintattun 'yan'uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi.Alheri da salamar Allah Ubanmu su tabbata a gare ku.

3. A kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Almasihu, duk sa'ad da muke yi muku addu'a,

4. saboda mun ji labarin bangaskiyarku ga Almasihu Yesu, da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan tsarkaka,

5. saboda bege ga abin da aka tanadar muku a sama. Kun riga kun ji labarin wannan a maganar gaskiya,

6. wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.

7. Haka ma kuka koya wurin Abafaras, ƙaunataccen abokin bautarmu. Shi amintaccen mai hidima ne na Almasihu a madadinmu,

8. ya kuma sanasshe mu ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.

9. Shi ya sa tun a ran da muka ji labarin, ba mu fāsa yi muku addu'a ba, muna roƙo a cika ku da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu,

Karanta cikakken babi Kol 1