Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Ku Ɗauki Wahalar Juna

1. Ya ku 'yan'uwa, in an kama mutum yana a cikin yin laifi, ku da kuke na ruhu, sai ku komo da shi a kan hanya da tawali'u, kowa yana kula da kansa kada shi ma ya burmu.

2. Ku ɗauki wahalar juna, ta haka za ku cika shari'ar Almasihu.

3. Kowa ya zaci shi wani abu ne, alhali kuwa shi ba kome ba ne, ya ruɗi kansa ke nan.

4. Kowa yă auna aikinsa ya gani, sa'an nan ne zai iya gadara da maƙaminsa shi da kansa, ba sai ya gwada kansa da wani ba.

5. Lalle kowa yă ji da kayansa.

6. Duk wanda aka koya wa Maganar, yă ci moriyar abubuwansa na alheri tare da mai koyarwa.

7. Kada fa a yaudare ku, ai, ba a iya zambatar Allah. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.

8. Wanda ya yi shuka a kwaɗayin son zuciyarsa, ta wurin son zuciya zai girbi ruɓa. Wanda ya yi shuka a Ruhu, ta wurin Ruhu zai girbi rai madawwami.

9. Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba.

10. To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda suke jama'ar masu ba da gaskiya ba.

Kashedi da kuma Gaisuwa

11. Ku dubi irin rubutu gwada-gwada da nake muku da hannuna!

12. To, mutanen nan masu son nuna bijinta cikin jiki, su ne masu son tilasta muku yin kaciya, don gudun shan wuya saboda gicciyen Almasihu.

13. Ai, ko waɗanda aka yi wa kaciya ma ba sa kiyaye Shari'a. Sonsu ne a yi muku kaciya, don su yi fāriya da ku a kan an yi muku kaciya.

14. Amma ni ko kusa ba zan yi fariya ba, sai dai a game da gicciyen Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta albarkacin mutuwarsa a kan gicciye ne na yar da sha'anin duniya, duniya kuma ta yar da sha'anina.

15. Kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba, sai dai sabuwar halitta ita ce wani abu.

16. Salama da jinƙai su tabbata ga duk masu bin ka'idar nan, wato Isra'ilar gaske ta Allah.

17. Daga nan gaba kada kowa ya ƙara damuna, domin a jikina ina da tabbai masu nuna ni bawan Ubangiji Yesu ne.

18. Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku, 'yan'uwa. Amin.