Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 5:16-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Maganata ita ce, ku yi zaman Ruhu, ba kuwa za ku biye wa halin mutuntaka ba.

17. Don halin mutuntaka gāba yake yi da Ruhu, Ruhu kuma yana gāba da halin mutuntaka. Waɗannan biyu gāba suke yi da juna, har ba kwa iya yin abin da kuke so.

18. In Ruhu ne yake bi da ku, ashe, Shari'a ba ta da iko da ku, ke nan.

19. Aikin halin mutuntaka a fili yake, wato, fasikanci, da aikin lalata, da fajirci,

20. da bautar gumaka, da sihiri, da gāba, da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da tsaguwa, da hamayya,

21. da hassada, da buguwa, da shashanci, da kuma sauran irinsu. Ina faɗakar da ku kamar yadda na faɗakar da ku a dā, cewa masu yin irin waɗannan abubuwa, ba za su sami gādo a Mulkin Allah ba.

22. Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci,

23. da tawali'u da kuma kamunkai. Masu yin irin waɗannan abubuwa, ba dama shari'a ta kama su.

24. Waɗanda kuwa suke su na Almasihu Yesu ne, sun gicciye halin mutuntaka da mugayen sha'awace-sha'awace iri iri.

25. In dai rayuwar tamu ta Ruhu ce, to, sai mu tafiyar da al'amuranmu ta wurin ikon Ruhu.

Karanta cikakken babi Gal 5