Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 5:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Almasihu ya 'yanta mu, 'yantawar gaske. Don haka sai ku dāge, kada ku sāke sarƙafewa a cikin ƙangin bauta.

2. To, ni Bulus, ina gaya muku, in kuna yarda a yi muku kaciya, Almasihu ba zai amfane ku kome ba ke nan.

3. Ina sāke tabbatar wa duk wanda ya yarda a yi masa kaciya, cewa wajibi ne ya bi dukkan Shari'a.

4. Ku da kuke neman kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, kun katse daga Almasihu ke nan, kun noƙe daga alherin Allah.

5. Gama mu, ta wurin ikon Ruhu, muke ɗokin cikar begen nan namu na samun adalcin Allah saboda bangaskiya.

6. In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.

Karanta cikakken babi Gal 5