Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 4:17-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Waɗannan suna habahaba da ku, amma ba da kyakkyawar niyya ba. Niyyarsu su raba ku da mu, don su ma ku yi habahaba da su.

18. Ai, in da kyakkyawar niyya, abu ne mai kyau koyaushe a yi habahaba da mutum, ba sai ina tare da ku kaɗai ba.

19. Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har Almasihu ya siffatu a zuciyarku!

20. Da ma a ce ina tare da ku a yanzu in sauya muryata! Gama na ruɗe a kan sha'aninku.

21. Ku gaya mini, ku da kuke son Shari'a ta yi iko da ku, ba kwa sauraron Sharia ne?

22. Domin a rubuce yake, Ibrahim yana da 'ya'ya biyu maza, ɗaya ɗan kuyanga, ɗaya kuma ɗan 'ya.

23. Ɗan kuyangar nan, an haife shi ne bisa ga ɗabi'a, ɗan 'yar kuwa ta cikar alkawarin ne.

24. Wannan kuwa duk don ishara ne, wato matan nan a kan alkawari biyu suke. Ɗaya tushensa Dutsen Sina'i, mai haihuwar bayi, wato Hajaratu ke nan.

25. To, ai, Hajaratu Dutsen Sina'i ce a ƙasar Larabawa. Ita ce kwatancin Urushalima ta yanzu, don ita da 'ya'yanta duk a bauta suke.

26. Amma Urushalima ta sama, ai 'ya ce, ita ce kuma uwarmu.

27. Domin a rubuce yake cewa,“ki yi farin ciki, ya ke bakarariya da ba kya haihuwa,Ki ɗauki sowa, ke da ba kya naƙuda,Don yasasshiya ta fi mai miji yawan 'ya'ya.”

28. To, 'yan'uwa, mu ma 'ya'yan alkawari ne kamar Ishaku.

29. Kamar yadda dā, shi da aka haifa bisa ga ɗabi'a ya tsananta wa wanda aka haifa bisa ga ikon Ruhun, haka a yanzu ma yake.

30. Amma me Nassin ya ce? “Ka kori kuyangar da ɗanta, don ko kaɗan ɗan kuyangar ba zai ci gādo tare da ɗan 'ya ba.”

Karanta cikakken babi Gal 4