Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 4:12-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Ina roƙonku, ya ku 'yan'uwana, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma in zama kamar yadda kuke. Ba ku taɓa yi mini wani laifi ba.

13. Kun dai sani a dalilin rashin lafiyata ne na yi muku bishara a zuwana na fari.

14. Ko da yake rashin lafiyata ta hana ku sukuni, duk da haka ba ku nuna mini raini ko ƙyama ba, sai dai kuka yi na'am da ni kamar wani mala'ikan Allah, ko ma Almasihu Yesu kansa.

15. To, ina daɗin nan da kuka ji a game da ni? Don na shaide ku a kan lalle da mai yiwuwa ne da kun ƙwaƙule idanunku kun ba ni!

16. Ashe, wato na zama abokin gābarku ne don na gaya muku gaskiya?

17. Waɗannan suna habahaba da ku, amma ba da kyakkyawar niyya ba. Niyyarsu su raba ku da mu, don su ma ku yi habahaba da su.

18. Ai, in da kyakkyawar niyya, abu ne mai kyau koyaushe a yi habahaba da mutum, ba sai ina tare da ku kaɗai ba.

19. Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har Almasihu ya siffatu a zuciyarku!

20. Da ma a ce ina tare da ku a yanzu in sauya muryata! Gama na ruɗe a kan sha'aninku.

21. Ku gaya mini, ku da kuke son Shari'a ta yi iko da ku, ba kwa sauraron Sharia ne?

22. Domin a rubuce yake, Ibrahim yana da 'ya'ya biyu maza, ɗaya ɗan kuyanga, ɗaya kuma ɗan 'ya.

23. Ɗan kuyangar nan, an haife shi ne bisa ga ɗabi'a, ɗan 'yar kuwa ta cikar alkawarin ne.

24. Wannan kuwa duk don ishara ne, wato matan nan a kan alkawari biyu suke. Ɗaya tushensa Dutsen Sina'i, mai haihuwar bayi, wato Hajaratu ke nan.

25. To, ai, Hajaratu Dutsen Sina'i ce a ƙasar Larabawa. Ita ce kwatancin Urushalima ta yanzu, don ita da 'ya'yanta duk a bauta suke.

26. Amma Urushalima ta sama, ai 'ya ce, ita ce kuma uwarmu.

Karanta cikakken babi Gal 4