Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 4:1-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ana nufin, magaji, muddin yana yaro bai fi bawa ba, ko da yake yana da mallakar dukkan kome.

2. A hannun iyayen goyo da wakilai yake har zuwa ranar da mahaifinsa ya sa.

3. Haka yake a gare mu, wato sa'ad da muke kamar yara, a cikin ƙangin bautar al'adun duniya muke.

4. Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiko Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe kuma a ƙarƙashin Shari'a,

5. domin ya fanso waɗanda suke a ƙarƙashin Shari'a, a mai da mu a matsayin 'ya'yan Allah.

6. Tun da yake ku 'ya'ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, yana kira, “Ya Abba! Uba!”

7. Don haka, kai ba bawa ba ne kuma, amma ɗa ne. Da yake ɗa ne kuma, to, magāji ne bisa ga ikon Allah.

8. Dā da ba ku san Allah ba, kuna bauta wa waɗansu gumaka, waɗanda ga ainihi ba a bakin kome suke ba.

9. Amma a yanzu da kuka san Allah, ko ma dai a ce Allah ya san ku, ta yaya za ku sāke komawa a kan raunanan al'adu marasa biyan bukata, har kuna neman komawa ga bautarsu?

10. Ga shi, al'adun ranaku, da na watanni, da na lokatai, da na shekaru ba sa wuce ku!

11. Amma kun ba ni tsoro, kada ya zamana na yi wahala a kanku a banza!

12. Ina roƙonku, ya ku 'yan'uwana, ku zama kamar yadda nake, domin ni ma in zama kamar yadda kuke. Ba ku taɓa yi mini wani laifi ba.

13. Kun dai sani a dalilin rashin lafiyata ne na yi muku bishara a zuwana na fari.

14. Ko da yake rashin lafiyata ta hana ku sukuni, duk da haka ba ku nuna mini raini ko ƙyama ba, sai dai kuka yi na'am da ni kamar wani mala'ikan Allah, ko ma Almasihu Yesu kansa.

15. To, ina daɗin nan da kuka ji a game da ni? Don na shaide ku a kan lalle da mai yiwuwa ne da kun ƙwaƙule idanunku kun ba ni!

16. Ashe, wato na zama abokin gābarku ne don na gaya muku gaskiya?

17. Waɗannan suna habahaba da ku, amma ba da kyakkyawar niyya ba. Niyyarsu su raba ku da mu, don su ma ku yi habahaba da su.

18. Ai, in da kyakkyawar niyya, abu ne mai kyau koyaushe a yi habahaba da mutum, ba sai ina tare da ku kaɗai ba.

Karanta cikakken babi Gal 4