Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 1:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. alhali kuwa ba wata bishara dabam, sai dai akwai waɗansu da suke ta da hankalinku, suna son jirkitar da bisharar Almasihu.

8. Amma ko mu, ko kuma wani mala'ika daga sama, in waninmu zai yi muku wata bishara dabam da wadda muka yi muku, to, ya zama la'ananne!

9. Kamar yadda muka faɗa a dā, haka yanzu ma nake sāke faɗa, cewa kowa ya yi muku wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, to, yă zama la'ananne!

10. To, wato ni son mutane nake nema ne, ko kuwa na Allah? Ko kuwa ƙoƙari nake yi in faranta wa mutane zuciya? Da har yanzu mutane nake faranta wa zuciya, ai, da ban zama bawan Almasihu ba.

11. Ina so in sanar da ku, 'yan'uwa, bisharar nan da na sanar ba ta ɗan adam ba ce,

12. domin ba daga wurin mutum na samo ta ba, ba kuma koya mini ita aka yi ba, sai dai ta wurin bayyanar Yesu Almasihu a gare ni ne na same ta.

13. Kun dai ji irin zamana na dā a cikin addinin yahudanci, yadda na riƙa tsananta wa Ikkilisiyar Allah ƙwarai da gaske, har ina ta watsa ta,

14. yadda kuma a cikin addinin Yahudanci har na tsere wa yawancin tsararrakina a cikin mutanenmu, na himmantu ƙwarai da gaske ga bin al'adun kakanninmu.

15. Amma sa'ad da shi wannan da ya keɓe ni tun kafin a haife ni, ya kuma kira ni bisa ga alherinsa, ya ji daɗin

16. bayyana Ɗansa a gare ni, domin in sanar da shi ga al'ummai, ban yi shawara da ɗan adam ba,

17. ban kuma je Urushalima wurin waɗanda suka riga ni zama manzanni ba, sai nan da nan na je ƙasar Larabawa, sa'an nan na komo Dimashƙu.

Karanta cikakken babi Gal 1