Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 1:6-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Na yi mamaki yadda nan da nan kuke ƙaurace wa wanda ya kira ku, bisa ga alherin Almasihu, har kuna koma wa wata baƙuwar bishara,

7. alhali kuwa ba wata bishara dabam, sai dai akwai waɗansu da suke ta da hankalinku, suna son jirkitar da bisharar Almasihu.

8. Amma ko mu, ko kuma wani mala'ika daga sama, in waninmu zai yi muku wata bishara dabam da wadda muka yi muku, to, ya zama la'ananne!

9. Kamar yadda muka faɗa a dā, haka yanzu ma nake sāke faɗa, cewa kowa ya yi muku wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, to, yă zama la'ananne!

Karanta cikakken babi Gal 1