Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Gal 1:11-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ina so in sanar da ku, 'yan'uwa, bisharar nan da na sanar ba ta ɗan adam ba ce,

12. domin ba daga wurin mutum na samo ta ba, ba kuma koya mini ita aka yi ba, sai dai ta wurin bayyanar Yesu Almasihu a gare ni ne na same ta.

13. Kun dai ji irin zamana na dā a cikin addinin yahudanci, yadda na riƙa tsananta wa Ikkilisiyar Allah ƙwarai da gaske, har ina ta watsa ta,

14. yadda kuma a cikin addinin Yahudanci har na tsere wa yawancin tsararrakina a cikin mutanenmu, na himmantu ƙwarai da gaske ga bin al'adun kakanninmu.

15. Amma sa'ad da shi wannan da ya keɓe ni tun kafin a haife ni, ya kuma kira ni bisa ga alherinsa, ya ji daɗin

16. bayyana Ɗansa a gare ni, domin in sanar da shi ga al'ummai, ban yi shawara da ɗan adam ba,

17. ban kuma je Urushalima wurin waɗanda suka riga ni zama manzanni ba, sai nan da nan na je ƙasar Larabawa, sa'an nan na komo Dimashƙu.

18. Bayan shekara uku kuma sai na tafi Urushalima ganin Kefas, na kuwa kwana goma sha biyar a gunsa.

19. Amma ban ga ko ɗaya a cikin sauran manzanni ba, sai dai Yakubu ɗan'uwan Ubangiji.

20. Abin nan da nake rubuto muku fa, ba ƙarya nake yi ba, a gaban Allah nake faɗa.

21. Daga baya kuma, na tafi ƙasar Suriya da ta Kilikiya.

22. Amma kuwa ikilisiyoyin Almasihu da suke a ƙasar Yahudiya, ba su san ni ido da ido ba tukuna.

23. Sai dai kawai sun ji an ce, “Wanda dā yake tsananta mana, ga shi, a yanzu yana sanar da bangaskiyar nan da dā yake ta rusawa!”

24. Sai suka ɗaukaka Allah saboda ni.

Karanta cikakken babi Gal 1