Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Filib 2:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. In akwai ƙarfafawa a cikin Almasihu, in dai da ƙarfin rinjaye na ƙauna, in har da tarayyarku ga Ruhu, da soyayyarku da kuma tausayinku,

2. to, albarkacinsu ku cikasa farin cikina da zamanku lafiya da juna, kuna ƙaunar juna, nufinku ɗaya, ra'ayinku ɗaya.

3. Kada ku yi kome da sonkai ko girmankai, sai dai da tawali'u, kowa yana mai da ɗan'uwansa ya fi shi.

4. Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula har da ta ɗan'uwansa ma.

5. Ku ɗauki halin Almasihu Yesu,

6. wanda, ko da yake a cikin surar Allah yake, bai mai da daidaitakar nan tasa da Allah abar da zai riƙe kankan ce ba,

7. sai ma ya mai da kansa baya matuƙa ta ɗaukar surar bawa, da kuma kasancewa da kamannin ɗan adam.

8. Da ya bayyana da siffar mutum, sai ya ƙasƙantar da kansa ta wurin yin biyayya, har wadda ta kai shi ga mutuwa, mutuwar ma ta gicciye.

9. Saboda haka ne kuma Allah ya ɗaukaka shi mafificiyar ɗaukaka, ya kuma yi masa baiwa da sunan nan da yake birbishin kowane suna,

Karanta cikakken babi Filib 2