Surori

  1. 1

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Fil 1 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Gaisuwa

1. Daga Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu, da kuma Timoti ɗan'uwanmu, zuwa ga Filiman ƙaunataccen abokin aikinmu,

2. da Aufiya 'yar'uwarmu, da Arkibus abokin famanmu, da kuma ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.

3. Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

Ƙaunar Filiman da Bangaskiyarsa

4. A kullum ina gode wa Allahna duk sa'ad da nake yi maka addu'a,

5. saboda nakan ji labarin ƙauna da bangaskiya da kake yi wa Ubangiji Yesu da dukkan tsarkaka.

6. Ina addu'a bangaskiyar nan da ta haɗa ku, tă kasance mai ƙwazo a wajen ciyar da sanin dukkan kyawawan abubuwan da suke namu, saboda Almasihu.

7. Na yi farin ciki ƙwarai, zuciyata kuma ta ƙarfafa saboda ƙaunar da kake yi, yă kai 'dan'uwana, domin zukatan tsarkaka sun wartsake ta dalilinka.

Bulus Ya Yi Roƙo domin Unisimas

8. Saboda haka, ko da yake saboda Almasihu ina iya umartarka gabagaɗi, ka yi abin da ya wajaba,

9. duk da haka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu,

10. ina roƙonka saboda ɗana Unisimas, wanda na zama ubansa ina ɗaure.

11. Dā kam, ba shi da wani amfani a wurinka, amma a yanzu, hakika yana da amfani a gare mu, ni da kai.

12. Ga shi nan, na komo maka da shi kamar gudan zuciyata.

13. Dā kam sona in riƙe shi a wurina, yă riƙa yi mini hidima a madadinka, muddin ina ɗaure saboda bishara.

14. Amma ba na so in yi kome ba tare da yardarka ba, don kada alherinka yă zamana na tilas ne, ba na ganin dama ba.

15. Watakila shi ya sa kuka ɗan rabu, don kă same shi har abada,

16. ba kuma a kan bawa ba, sai dai a kan abin da ya fi bawa, wato 'dan'uwa abin ƙauna, tun ba ma a gare ni ba, balle fa a gare ka, ta wajen al'amarin jiki da kuma wajen al'amarin Ubangiji.

17. Saboda haka in ka ɗauke ni a kan abokin tarayya, to, sai ka karɓe shi kamar yadda za ka karɓe ni.

18. Ko ma ya yi maka wani laifi, ko kuwa kana binsa wani abu, sai ka mai da shi a kaina.

19. Ni Bulus, ni nake rubuto wannan da hannuna, ni kuwa zan biya, kada ma a yi zancen ranka da na fanso maka!

20. Ya ɗan'uwana, ka yarda in sami wata fa'ida a gare ka saboda Ubangiji! Ka sanyaya mini zuciya saboda Almasihu.

21. Don na tabbatar da biyayyarka, shi ya sa na rubuto maka, don na sani za ka yi, har fiye da abin da na faɗa.

22. Har wa yau kuma, ka shirya mini masauki, domin ina sa zuciya a ba ni yarjin zuwa gare ku albarkacin addu'arku.

Gaisuwa

23. Abafaras, abokin ɗaurina saboda Almasihu Yesu, yana gaishe ka,

24. haka kuma Markus, da Aristarkus, da Dimas, da Luka, abokan aikina, suna gaishe ka.

25. Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a zukatanku.