Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 8:5-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Filibus ya tafi birnin Samariya, yana ta yi musu wa'azin Almasihu.

6. Da taron suka ji, suka kuma ga mu'ujizan da Filibus yake yi, da nufi ɗaya suka mai da hankali ga abin da ya faɗa.

7. Domin da yawa masu baƙaƙen aljannu suka rabu da su, aljannun kuwa na ta ihu. Shanyayyu da guragu da yawa kuma an warkar da su.

8. Saboda haka aka yi ta farin ciki a garin ƙwarai da gaske.

9. Akwai wani mutum kuwa, mai suna Saminu, wanda dā yake sihiri a birnin, har yana ba Samariyawa mamaki, yana cewa shi wani muhimmi ne.

10. Duk jama'a kuwa suka mai da hankali a gare shi, babba da yaro, suna cewa, “Mutumin nan, ai, ikon nan ne na Allah, da ake kira mai girma.”

11. Sai suka mai da hankali gare shi, don ya daɗe yana ta ba su al'ajabi da sihirinsa.

12. Amma da suka gaskata bisharar da Filibus ya yi a kan Mulkin Allah, da kuma sunan Yesu Almasihu, duka aka yi musu baftisma mata da maza.

13. Har Saminu da kansa ma ya ba da gaskiya, bayan an yi masa baftisma kuma ya manne wa Filibus. Ganin kuma ana yin mu'ujizai da manyan al'ajibai, ya yi mamaki ƙwarai.

14. To, da manzannin da suke Urushalima suka ji Samariyawa sun yi na'am da Maganar Allah, suka aika musu da Bitrus da Yahaya.

15. Su kuwa da suka iso, suka yi musu addu'a don su sami Ruhu Mai Tsarki,

16. domin bai sauko wa ko wannensu ba tukuna, sai dai kawai an yi musu baftisma ne da sunan Ubangiji Yesu.

17. Sai suka ɗora musu hannu, suka kuwa sami Ruhu Mai Tsarki.

18. To, da Saminu ya ga, ashe, ta ɗora hannun manzanni ne ake ba da Ruhun, sai ya miƙa musu kuɗi,

19. ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iko, don kowa na ɗora wa hannu, yă sami Ruhu Mai Tsarki.”

20. Amma Bitrus ya ce masa, “Ku hallaka, kai da kuɗinka, don ka zaci da kuɗi ne za ka sami baiwar Allah!

21. Ba ruwanka da wannan al'amari sam, don zuciyarka ba ɗaya take ba a gaban Allah.

22. Saboda haka sai ka tuba da wannan mugun aiki naka, ka roƙi Ubangiji ko a gafarta maka abin da ka riya a zuciyarka.

Karanta cikakken babi A.m. 8