Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 8:29-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa ka yi kusa da keken dokin nan.”

30. Sai Filibus ya yi gudu zuwa wurinsa, ya ji shi yana karatun littafin Annabi Ishaya. Ya ce, “Kana kuwa fahimtar abin da kake karantawa?”

31. Sai ya ce, “Ina fa? Sai ko wani ya fassara mini.” Sai ya roƙi Filibus ya hau su zauna tare.

32. Wannan kuwa shi ne nassin da yake karantawa, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka. Kamar yadda ɗan rago yake shiru a hannun mai sausayarsa, Haka, ko bakinsa bai buɗe ba.

33. An yi masa ƙasƙanci har an hana masa gaskiya tasa. Wa yake iya ba da labarin zamaninsa? Domin an katse ransa daga duniya.”

34. Sai bābān ya ce wa Filibus, “Shin kam, annabin nan, maganar wa yake yi? Tasa ko ta wani?”

35. Sai Filibus ya buɗe baki ya fara da wannan Nassi, yana yi masa bisharar Yesu.

36. Suna cikin tafiya, suka iso wani ruwa, sai bābān ya ce, “Ka ga ruwa! Me zai hana a yi mini baftisma?”

37. Filibus ya ce, “In dai ka ba da gaskiya da zuciya ɗaya, ai, sai a yi maka.” Bābān ya amsa ya ce, “Na gaskata Yesu Almasihu ɗan Allah ne.”

38. Sai ya yi umarni a tsai da keken dokin. Sai dukansu biyu suka gangara cikin ruwan, Filibus da bābān, ya yi masa baftisma.

39. Da suka fito daga ruwan, Ruhun Ubangiji ya fauce Filibus, bābān kuma bai ƙara ganinsa ba. Sai ya yi ta tafiya tasa yana farin ciki.

40. Amma aka ga Filibus a Azotus. Sai ya zaga dukan garuruwa, yana yin bishara, har ya isa Kaisariya.

Karanta cikakken babi A.m. 8