Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 8:18-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. To, da Saminu ya ga, ashe, ta ɗora hannun manzanni ne ake ba da Ruhun, sai ya miƙa musu kuɗi,

19. ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iko, don kowa na ɗora wa hannu, yă sami Ruhu Mai Tsarki.”

20. Amma Bitrus ya ce masa, “Ku hallaka, kai da kuɗinka, don ka zaci da kuɗi ne za ka sami baiwar Allah!

21. Ba ruwanka da wannan al'amari sam, don zuciyarka ba ɗaya take ba a gaban Allah.

22. Saboda haka sai ka tuba da wannan mugun aiki naka, ka roƙi Ubangiji ko a gafarta maka abin da ka riya a zuciyarka.

23. Domin na ga kai tushen ɗaci ne, kana kulle a cikin mugunta.”

24. Sai saminu ya amsa ya ce, “Ku roƙar mini Ubangiji kada ko ɗaya daga cikin abin da kuka faɗa ya aukar mini.”

25. To, bayan manzannin sun tabbatar da Maganar Ubangiji, sun faɗe ta, suka koma Urushalima, suna yin bishara a ƙauyukan Samariyawa da yawa.

26. Sai wani mala'ikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Tashi, ka yi kudu, ka bi hanyar da ta fito daga Urushalima zuwa Gaza,” wato hanyar hamada.

27. Sai ya tashi ya tafi. Ga wani mutumin Habasha, wani bābā, mai babban matsayi a mulkin Kandakatu, sarauniyar Habasha, shi ne kuwa ma'ajinta, ya zo Urushalima ne yin sujada,

28. yana komawa gida a zaune a cikin keken dokinsa, yana karatun littafin Annabi Ishaya.

29. Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa ka yi kusa da keken dokin nan.”

30. Sai Filibus ya yi gudu zuwa wurinsa, ya ji shi yana karatun littafin Annabi Ishaya. Ya ce, “Kana kuwa fahimtar abin da kake karantawa?”

31. Sai ya ce, “Ina fa? Sai ko wani ya fassara mini.” Sai ya roƙi Filibus ya hau su zauna tare.

32. Wannan kuwa shi ne nassin da yake karantawa, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka. Kamar yadda ɗan rago yake shiru a hannun mai sausayarsa, Haka, ko bakinsa bai buɗe ba.

Karanta cikakken babi A.m. 8