Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 8:12-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Amma da suka gaskata bisharar da Filibus ya yi a kan Mulkin Allah, da kuma sunan Yesu Almasihu, duka aka yi musu baftisma mata da maza.

13. Har Saminu da kansa ma ya ba da gaskiya, bayan an yi masa baftisma kuma ya manne wa Filibus. Ganin kuma ana yin mu'ujizai da manyan al'ajibai, ya yi mamaki ƙwarai.

14. To, da manzannin da suke Urushalima suka ji Samariyawa sun yi na'am da Maganar Allah, suka aika musu da Bitrus da Yahaya.

15. Su kuwa da suka iso, suka yi musu addu'a don su sami Ruhu Mai Tsarki,

16. domin bai sauko wa ko wannensu ba tukuna, sai dai kawai an yi musu baftisma ne da sunan Ubangiji Yesu.

17. Sai suka ɗora musu hannu, suka kuwa sami Ruhu Mai Tsarki.

18. To, da Saminu ya ga, ashe, ta ɗora hannun manzanni ne ake ba da Ruhun, sai ya miƙa musu kuɗi,

19. ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iko, don kowa na ɗora wa hannu, yă sami Ruhu Mai Tsarki.”

20. Amma Bitrus ya ce masa, “Ku hallaka, kai da kuɗinka, don ka zaci da kuɗi ne za ka sami baiwar Allah!

21. Ba ruwanka da wannan al'amari sam, don zuciyarka ba ɗaya take ba a gaban Allah.

22. Saboda haka sai ka tuba da wannan mugun aiki naka, ka roƙi Ubangiji ko a gafarta maka abin da ka riya a zuciyarka.

23. Domin na ga kai tushen ɗaci ne, kana kulle a cikin mugunta.”

Karanta cikakken babi A.m. 8