Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 8:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Shawulu kuwa yana goyon bayan kisan Istifanas.A ran nan kuwa wani babban tsanani ya auko wa Ikkilisiyar da take Urushalima. Duk aka warwatsa su a lardin Yahudiya da na Samariya, sai dai manzannin kawai.

2. Sai waɗansu mutane masu bautar Allah suka binne Istifanas, suka yi masa kuka ƙwarai.

3. Amma Shawulu ya yi ta yi wa Ikkilisiya ɓarna ƙwarai da gaske, yana shiga gida gida, yana jan mata da maza, yana jefa su a kurkuku.

4. To, waɗanda aka warwatsar nan kuwa, suka yi ta zazzagawa suna yin bishara.

5. Filibus ya tafi birnin Samariya, yana ta yi musu wa'azin Almasihu.

6. Da taron suka ji, suka kuma ga mu'ujizan da Filibus yake yi, da nufi ɗaya suka mai da hankali ga abin da ya faɗa.

7. Domin da yawa masu baƙaƙen aljannu suka rabu da su, aljannun kuwa na ta ihu. Shanyayyu da guragu da yawa kuma an warkar da su.

8. Saboda haka aka yi ta farin ciki a garin ƙwarai da gaske.

Karanta cikakken babi A.m. 8