Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 7:55-60 Littafi Mai Tsarki (HAU)

55. Amma Istifanas, a cike da Ruhu Mai Tsarki, sai ya zuba ido sama, ya ga ɗaukakar Allah, da kuma Yesu tsaye a dama ga Allah.

56. Sai ya ce, “Ga shi, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗan Mutum tsaye dama ga Allah.”

57. Amma suka ɗauki ihu ƙwarai, suka tattoshe kunnuwansu, suka aukar masa da nufi ɗaya,

58. suka fitar da shi a bayan gari suka yi ta jifansa da dutse. Shaidu kuwa suka ajiye tufafinsu wurin wani saurayi, wai shi Shawulu.

59. Suna ta jifan Istifanas, shi kuwa yana ta addu'a, yana cewa, “Ya Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”

60. Sa'an nan ya durƙusa, ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Ya Ubangiji, kada ka ɗora musu wannan zunubi.” Da faɗar haka sai ya yi barci.

Karanta cikakken babi A.m. 7