Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 7:11-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. To, sai wata yunwa ta auku a dukan ƙasar Masar da ta Kan'ana, game da matsananciyar wahala, har kakanninmu suka rasa abinci.

12. Amma da Yakubu ya ji akwai alkama a Masar, ya aiki kakanninmu tafiyar farko.

13. A tafiyarsu ta biyu Yusufu ya sanar da kansa ga 'yan'uwansa, asalinsa kuma ya sanu ga Fir'auna.

14. Sai Yusufu ya aika wa ubansa Yakubu yă zo, da kuma dukan 'yan'uwansa, mutum saba'in da biyar.

15. Sai Yakubu ya tafi Masar. A can ma ya mutu, shi da kakanninmu.

16. Sai aka ɗebo su aka mai da su Shekem, aka sa su a kabarin da Ibrahim ya saya da kuɗi azurfa a wurin 'ya'yan Hamor a nan Shekem.

17. “Amma da lokacin cikar alkawarin da Allah ya yi wa Ibrahim ya gabato, jama'ar suka ƙaru, suka yawaita ƙwarai a ƙasar Masar,

18. har aka yi wani sarki a Masar, wanda bai san ko wane ne Yusufu ba.

19. Wannan sarki kuwa ya cuci kabilarmu, yana gwada wa kakanninmu tasku, yana sawa a yar da jariransu, don kada su rayu.

20. A lokacin nan ne aka haifi Musa, yaro kyakkyawan gaske. Sai aka rene shi wata uku a gidan ubansa.

21. Da aka yar da shi waje, 'yar Fir'auna ta ɗauke shi tallafinta, ta goya shi kamar ɗanta.

22. Sai aka karantar da Musa dukan ilimin Masarawa, shi kuwa mutum mai iko ne a cikin magana da ayyukansa.

23. “Yana gab da cika shekara arba'in ke nan, sai ya faɗo masa a rai yă ziyarci 'yan'uwansa Isra'ilawa.

24. Da ya ga ana cutar ɗayansu, ya tare wanda ake wulakantawa, ya rama masa, ya buge Bamasaren, ya mutu.

25. Ya zaci 'yan'uwansa sun gane ta hannunsa ne Allah zai cece su. Amma ba su gane ba.

26. Kashegari kuma waɗansu suna faɗa, sai ya nemi shirya su, ya ce, ‘Ku jama'a, ku 'yan'uwa ne fa, don me kuke cutar juna?’

27. Amma mai cutar ɗan'uwa nasa ya ture Musa, ya ce, ‘Wa ya sa ka shugaba da alƙali a kanmu?

Karanta cikakken babi A.m. 7