Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 7:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai babban firist ya ce, “Ashe, haka ne?”

2. Sai Istifanas ya ce, “Ya ku 'yan'uwa da shugabanni, ku saurare ni. Allah Maɗaukaki ya bayyana ga kakanmu Ibrahim, sa'ad da yake ƙasar Bagadaza, tun bai zauna a Haran ba,

3. ya ce masa, ‘Tashi daga ƙasarku, daga kuma cikin 'yan'uwanka, ka je ƙasar da zan nuna maka.’

4. Sai ya tashi daga ƙasar Kaldiyawa, ya zauna a Haran. Daga can kuma, bayan mutuwar tsohonsa, Allah ya kawo shi ƙasar nan da yanzu kuke zaune.

5. Amma kuwa shi kansa, bai ba shi gādonta ba, ko da taki ɗaya, sai dai ya yi masa alkawari zai mallakar masa ita, shi da zuriyar bayansa, ko da yake ba shi da ɗa a lokacin.

6. Abin da Allah ya faɗa kuwa shi ne zuriyar Ibrahim za su yi baƙunci a wata ƙasa, mutanen ƙasar kuwa za su bautar da su, su kuma gwada musu tasku har shekara arbaminya.

7. ‘Har wa yau kuma,’ Allah ya ce, ‘Al'ummar da za su bauta wa, ni zan hukunta ta, bayan haka kuma za su fito su bauta mini a wannan wuri.’

8. Ya kuma yi masa alkawari game da kaciya. Ta haka, da Ibrahim ya haifi Ishaku, ya yi masa kaciya a rana ta takwas. Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi kakanninmu sha biyun nan.

9. “Kakannin nan kuwa, da yake suna kishin Yusufu, suka sayar da shi, aka kai shi Masar. Amma Allah na tare da shi,

10. ya kuma tsamo shi daga dukan wahala tasa, ya ba shi farin jini da hikima a gun Fir'auna, Sarkin Masar, shi kuwa ya naɗa shi mai mulkin Masar, ya kuma danƙa masa jama'ar gidansa duka.

11. To, sai wata yunwa ta auku a dukan ƙasar Masar da ta Kan'ana, game da matsananciyar wahala, har kakanninmu suka rasa abinci.

Karanta cikakken babi A.m. 7