Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 6:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sa'an nan waɗansu na majami'ar da ake kira majami'ar Libartinawa, wato Kuraniyawa da Iskandariyawa, da kuma waɗansu daga ƙasar Kilikiya da ta Asiya, suka tasar wa Istifanas da muhawwara.

10. Amma ko kaɗan ba dama su yi masa mūsu, domin ya yi magana da hikima, Ruhu na iza shi.

11. Sai suka zuga mutane a asirce, su kuwa suka ce, “Mun ji shi yana zagin Musa, yana saɓon Allah.”

12. Ta haka suka ta da hankalin jama'a, da shugabanni, da malaman Attaura, su kuma suka aukar masa, suka kama shi, suka kawo shi a gaban majalisa.

13. Sai suka gabatar da masu shaidar zur, suka ce, “Mutumin nan ba ya rabuwa da kushe tsattsarkan wurin nan, da kuma Attaura,

14. don mun ji shi yana cewa wai wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan, yă kuma sauya al'adun da Musa ya bar mana.”

15. Da duk waɗanda suke zaune a majalisar suka zura masa ido, suka ga fuska tasa kamar fuskar mala'ika take.

Karanta cikakken babi A.m. 6