Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 4:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Suna cikin yin magana da jama'a sai firistoci da shugaban dogaran Haikali da Sadukiyawa suka ji haushi ƙwarai, suka aukar musu,

2. don suna koya wa jama'a, suna tabbatar da tashi daga matattu, suna misali da Yesu.

3. Sai suka kama su, suka sa su a gidan waƙafi kafin gobe, don magariba ta riga ta yi.

4. Amma da yawa daga cikin waɗanda suka ji wa'azin sun ba da gaskiya, har jimillarsu ta kai wajen mutum dubu biyar.

5. Kashegari shugabanninsu da dattawansu da malamansu na Attaura suka taru a Urushalima,

6. tare da Hanana, babban firist, da Kayafa, da Yahaya, da Iskandari, da kuma duk waɗanda suke dangin babban firist.

7. Da suka tsai da su a tsakiya, suka tuhume su, suka ce, “Da wane iko ne, ko kuwa da wane suna ne, kuka yi haka?”

8. Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya ce musu, “Ya ku shugabannin jama'a, da dattawa,

9. in dai ana tuhumarmu ne yau a kan alherin da aka yi wa gajiyayyen mutumin nan, ta yadda aka warkar da shi,

10. to, sai ku sani, ku duka, da kuma duk jama'ar Isra'ila, da sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda ku kuka gicciye, wanda kuma Allah ya tashi shi daga matattu, albarkacinsa ne mutumin nan yake tsaye a gabanku lafiyayye.

11. Wannan shi ne dutsen nan da ku magina kuka raina, shi ne kuwa ya zama mafificin dutsen gini.

12. Ba kuma samun ceto ga wani, domin ba wani suna duk duniyan nan da aka bayar cikin mutane, wanda lalle ta wurinsa ne za mu sami ceto.”

Karanta cikakken babi A.m. 4