Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 27:24-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. ya ce, ‘Kada ka ji tsoro Bulus, lalle za ka tsaya a gaban Kaisar, ga shi kuma, Allah ya amsa ya yardar maka duk abokan tafiyarka su tsira.’

25. Saboda haka, sai ku yi ƙarfin hali, ya ku jama'a, domin na gaskata Allah a kan cewa, yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka za a yi.

26. Amma fa lalle ne a fyaɗa mu a wani tsibirin.”

27. A dare na goma sha huɗu, ana ta kora mu sakaka a bahar Adariya, wajen tsakar dare sai masu tuƙi suka zaci mun yi kusa da ƙasa.

28. Sai suka gwada zurfin ruwan, suka sami gaba ashirin, da muka ci gaba kaɗan, sai suka sāke gwadawa, suka sami gaba goma sha biyar.

29. Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki anka guda huɗu na bayan jirgin, suka ƙagauta gari ya waye.

30. Masu tuƙi suna neman gudu daga jirgin ke nan, har sun zura ƙaramin jirgi a cikin ruwa, wai don a ga kamar za su ja su anka ɗin ne daga goshin jirgin su sake su,

31. sai Bulus ya ce da jarumin yaki da kuma sojan. “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba yadda za a yi ku tsira.”

32. Sai sojan suka yayyanke igiyoyin ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.

33. Da gari ya yi kusan wayewa sai Bulus ya roƙe su su taɓa ɗan abinci, ya ce, “Yau fa kwana goma sha huɗu ke nan kuke zaman jira, ba wani abin da kuka ci.

34. Saboda haka, ina roƙonku ku ci abinci, don lafiyarku, tun da yake ba wanda ko gashin kansa zai yi ciwo a cikinku.”

35. Da ya faɗi haka, ya ɗauki curin gurasa, ya yi godiya ga Allah a gabansu duka, sa'an nan ya gutsuttsura ya fara ci.

Karanta cikakken babi A.m. 27