Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 27:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da aka shirya mu tashin jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya, sai suka danƙa Bulus da waɗansu 'yan sarƙa a hannun wani jarumi, mai suna Yuliyas, na ƙungiyar Augustas.

2. Da muka shiga wani jirgi na Adaramitiya, mai shirin tashi zuwa waɗansu garuruwan da suke gaɓar Asiya, muka fara tafiya. Aristarkus kuwa, wani mutumin Tasalonika ta ƙasar Makidoniya, na tare da mu.

3. Kashegari ga mu a Sidon. Yuliyas kuwa ya yi wa Bulus alheri, ya ba shi izini ya je ya gano abokansa, su yi masa taimako.

4. Da muka tashi daga nan a jirgin ruwa sai muka zaga ta bayan tsibirin Kubrus, saboda iska tana gāba da mu.

Karanta cikakken babi A.m. 27