Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 22:5-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Babban firist ma da dukan majalisar shugabannin jama'a za su iya shaidata, daga gunsu ne kuma na karɓi wasiƙu zuwa ga 'yan'uwanmu Yahudawa, na tafi Dimashƙu, don in ɗebo waɗanda suke can ma, in zo da su Urushalima a ɗaure, a azabta su.”

6. “Ina cikin tafiya, da na yi kusa da Dimashƙu, wajen rana tsaka, kwamfa sai wani matsanancin haske ya bayyano daga sama, ya haskaka kewaye da ni.

7. Sai na fāɗi, na kuma ji wata murya tana ce mini, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?’

8. Ni kuma na amsa na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ Sai ya ce mini, ‘Ni ne Yesu Banazare wanda kake tsananta wa.’

9. To, waɗanda suke tare da ni sun ga hasken, amma ba su ji kalmomin mai yi mini maganar nan ba.

10. Sai na ce, ‘To, me zan yi, ya Ubangiji?’ Sai ubangiji ya ce mini, ‘Tashi, ka shiga Dimashƙu, a can ne za a faɗa maka duk abin da aka ɗora maka ka yi.’

11. Da na kāsa gani saboda tsananin hasken nan, sai waɗanda suke tare da ni suka yi mini jagora, har na isa Dimashƙu.

12. “Sai kuma wani mai suna Hananiya, mai bautar Allah ne wajen bin Shari'a, wanda duk Yahudawan da suke zaune a can suke yabo,

13. ya zo ya tsaya a kusa da ni, ya ce mini, ‘Ya ɗan'uwana Shawulu, ganinka yă komo maka.’ Nan tāke, sai ganina ya komo, na kuwa gan shi.

14. Sai ya ce, ‘Allahn kakanninmu ya zaɓe ka don kă san nufinsa, ka ga Mai Adalcin nan, ka kuma ji jawabi daga bakinsa.

15. Don za ka zama mashaidinsa ga dukan mutane game da abin da ka gani, ka kuma ji.

16. To, a yanzu me kake jira? Tashi, a yi maka baftisma a wanke zunubanka ta wurin kira bisa sunansa.’ ”

17. “Da na komo Urushalima, ina addu'a a Haikali, sai wahayi ya zo mini.

18. Na gan shi, yana ce mini, ‘Yi sauri maza ka fita daga Urushalima, don ba za su yarda da shaidarka a kaina ba.’

Karanta cikakken babi A.m. 22