Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 20:26-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Saboda haka ina dai tabbatar muku a yau, cewa na kuɓuta daga hakkin kowa,

27. domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.

28. Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.

29. Na sani bayan tashina waɗansu mugayen kyarketai za su shigo a cikinku, ba kuwa za su ji tausayin garken ba.

30. Har ma a cikinku waɗansu mutane za su taso, suna maganganun da ba sa kan hanya, don su jawo masu bi gare su.

31. Saboda haka sai ku zauna a faɗake, ku tuna, shekara uku ke nan ba dare ba rana, ban fasa yi wa kowa gargaɗi ba, har da hawaye.

32. To, yanzu na danƙa ku ga Ubangiji, maganar alherinsa kuma tă kiyaye ku, wadda ita take da ikon inganta ku, ta kuma ba ku gādo tare da dukan tsarkaka.

33. Ban yi ƙyashin kuɗin kowa ba, ko kuwa tufafin wani.

34. Ku da kanku kun sani hannuwan nan nawa su suka biya mini bukace-bukacena, da na waɗanda suke tare da ni.

35. Na zamar muku abin misali ta kowace hanya, cewa ta wahalar aiki haka lalle ne a taimaki masu ƙaramin ƙarfi, kuna kuma tunawa da Maganar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”

Karanta cikakken babi A.m. 20