Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 20:21-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. ina tabbatar wa Yahudawa da al'ummai duka sosai wajibcin tuba ga Allah, da kuma gaskatawa da Ubangijinmu Yesu.

22. To, ga shi kuma, yanzu zan tafi Urushalima, Ruhu yana iza ni, ban kuwa san abin da zai same ni a can ba,

23. sai dai Ruhu Mai Tsarki yakan riƙa tabbatar mini a kowane gari, cewa ɗauri da shan wuya na dākona.

24. Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.

25. To, ga shi, yanzu na san dukanku ba za ku ƙara ganina ba, ku da na zazzaga cikinku ina yi muku bisharar Mulkin Allah.

26. Saboda haka ina dai tabbatar muku a yau, cewa na kuɓuta daga hakkin kowa,

27. domin ban ji nauyin sanar da ku dukan nufin Allah ba.

28. Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.

29. Na sani bayan tashina waɗansu mugayen kyarketai za su shigo a cikinku, ba kuwa za su ji tausayin garken ba.

30. Har ma a cikinku waɗansu mutane za su taso, suna maganganun da ba sa kan hanya, don su jawo masu bi gare su.

31. Saboda haka sai ku zauna a faɗake, ku tuna, shekara uku ke nan ba dare ba rana, ban fasa yi wa kowa gargaɗi ba, har da hawaye.

32. To, yanzu na danƙa ku ga Ubangiji, maganar alherinsa kuma tă kiyaye ku, wadda ita take da ikon inganta ku, ta kuma ba ku gādo tare da dukan tsarkaka.

Karanta cikakken babi A.m. 20