Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 2:38-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa ko wannenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki,

39. domin alkawarin nan ku aka yi wa, ku da 'ya'yanku, da kuma dukan manisanta, wato duk waɗanda Ubangiji Allahnmu ya kira.”

40. Sai ya yi ta tabbatar musu da maganganu masu yawa, yana ta yi musu gargaɗi, yana cewa, “Ku tsirar da kanku daga wannan karkataccen zamani.”

41. Waɗanda suka ya na'am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku.

42. Sai suka himmantu ga koyarwar manzanni da tarayya da juna, da gutsuttsura gurasa, da kuma yin addu'a.

43. Sai tsoro ya kama kowa, aka kuma yi abubuwan al'ajabi da mu'ujizai da yawa ta wurin manzannin.

44. Dukan masu ba da gaskiya suna tare, suna mallakar kome nasu gaba ɗaya.

45. Suka sayar da mallakarsu da kayansu, suka rarraba wa kowa kuɗin, gwargwadon bukatarsa.

46. Kowace rana kuma sukan riƙa zuwa Haikali da nufi ɗaya, suna gutsuttsura gurasa a gidajensu, suna cin abinci da farin ciki ƙwarai, rai kwance,

47. suna yabon Allah, suna da farin jini a wurin dukan mutane. Kowace rana kuma Ubangiji yana ƙara masu waɗanda ake ceta.

Karanta cikakken babi A.m. 2