Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 2:24-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Amma Allah ya tashe shi bayan ya ɓalle masa ƙangin mutuwa, domin ba shi yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.

25. Dawuda kuma ya yi faɗi a game da shi ya ce,‘Kullum hankalina yana kan Ubangiji,Yana damana, domin kada in jijjigu.

26. Saboda haka, zuciyata ta yi fari, ina farin ciki matuƙa.Ko da yake kuma ni jiki ne, zan zauna ina sa zuciya,

27. Domin ba za ka yar da raina a Hades ba,Ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.

28. Kā sanar da ni hanyoyin rai.Za ka cika ni da farin ciki ta zamana a zatinka.’

29. Ya 'yan'uwa, na iya yi muku magana da amincewa a game da kakanmu Dawuda, cewa ya mutu, an binne shi, kabarinsa kuma yana nan gare mu har ya zuwa yau.

30. To, da yake shi annabi ne, ya kuma san Allah ya rantse masa, cewa zai ɗora wani daga cikin zuriya tasa kan kursiyinsa,

31. sai ya hango, ya kuma yi faɗi a kan tashin Almasihu daga matattu, cewa ba za a yashe shi a Hades ba, jikinsa kuwa ba zai ruɓa ba.

32. Yesun nan kam, Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa duk shaidu ne ga haka.

33. Da yake an ɗaukaka shi a dama ga Allah, ya kuma sami cikar alkawarin nan na baiwar Ruhu Mai Tsarki daga wurin Uba, sai ya zubo da wannan da kuke gani, kuke kuma ji.

34. Ai, ba Dawuda ne ya hau Sama ba, amma shi kansa ya ce,‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,Zauna a damana,

35. Sai na sa ka take maƙiyanka.’

36. “Don haka sai duk jama'ar Isra'ila su sakankance, cewa shi Yesun na da kuka gicciye, Allah ya mai da shi Ubangiji, da kuma Almasihu.”

37. To, da suka ji haka, maganar ta soke su a zuci, suka ce wa Bitrus da sauran manzannin, “'Yan'uwa, me za mu yi?”

38. Sai Bitrus ya ce musu, “Sai ku tuba, a yi wa ko wannenku baftisma, a kan kun yarda da sunan Yesu Almasihu, domin a gafarta zunubanku, za ku kuwa sami baiwar Ruhu Mai Tsarki,

39. domin alkawarin nan ku aka yi wa, ku da 'ya'yanku, da kuma dukan manisanta, wato duk waɗanda Ubangiji Allahnmu ya kira.”

Karanta cikakken babi A.m. 2