Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 2:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da ranar Fentikos ta yi, duk suna tare a wuri ɗaya,

2. farat ɗaya, sai aka ji wani amo daga sama, kamar na busowar gawurtacciyar iska, ya cika duk gidan da suke zaune.

3. Sai waɗansu harsuna kamar na wuta suka bayyana a gare su, suna rarrabuwa, suna sassauka a kan ko wannensu.

4. Sai duk, aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka kuma fara magana da waɗansu harsuna dabam dabam, gwargwadon yadda Ruhun ya yi musu baiwar yin magana.

5. To, a Urushalima a lokacin, akwai waɗansu Yahudawa masu bautar Allah daga ko'ina cikin ƙasashen duniya.

6. Da jin dirin nan kuwa, taron ya haɗe, ya ruɗe, domin ko wannensu ya ji suna magana da bakin garinsu.

7. Sai suka yi al'ajabi suka yi mamaki, suna cewa, “Ashe, duk masu maganar nan ba Galilawa ba ne?

8. Ƙaƙa kuwa ko wannenmu yake ji da bakin garinsu ake magana?

9. Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Madayanawa, da Elamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya,

10. da na Firijiya, da na Bamfiliya, da na Masar, da kuma na kewayen Kurane ta ƙasar Libiya, har ma da baƙi daga Roma, wato Yahudawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci,

Karanta cikakken babi A.m. 2