Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 16:25-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. A wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu'a suna waƙoƙin yabon Allah, 'yan sarka kuwa suna sauraronsu,

26. farat ɗaya, sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, har harsashin ginin kurkuku ya raurawa. Nan da nan ƙofofin suka bubbuɗe, marin kowa kuma ya ɓalle.

27. Da yāri ya farka daga barci ya ga ƙofofin kurkuku a buɗe, ya zaro takobinsa, yana shirin kashe kansa, cewa yake 'yan sarƙa sun gudu.

28. Amma Bulus ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Kada ka cuci kanka, ai duk muna nan!”

29. Sai yari ya ce a kawo fitilu, ya yi wuf ya ruga ciki, ya fāɗi gaban Bulus da Sila, yana rawar jiki don tsoro.

30. Sa'an nan ya fito da su waje, ya ce, “Ya shugabanni, me zan yi in sami ceto?”

31. Su kuwa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”

32. Sa'an nan suka gaya masa Maganar Ubangiji, shi da iyalinsa duka.

33. Nan take da daddaren nan ya ɗebe su, ya wanke musu raunukansu. Nan da nan kuwa aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa.

34. Sa'an nan ya kawo su gidansa, ya kawo musu abinci, ya yi ta farin ciki matuƙa, domin shi da iyalinsa duka sun gaskata da Allah.

35. Amma da gari ya waye, sai alƙalan suka aiko dogarai, suka ce, “Suka ce a saki mutanen nan.”

36. Yari kuwa ya shaida wa Bulus maganar, ya ce, “Alƙalai sun aiko a sake ku, saboda haka yanzu sai ku fito, ku tafi lafiya.”

37. Amma Bulus ya ce musu, “Ai, a fili suka daddoke mu, ba ko bin ba'asi, mu ma da muke Romawa bisa ga 'yangaranci, suka jefa mu a kurkuku, yanzu kuma sā fitar da mu a ɓoye? Sai dai su zo da kansu su fito da mu.”

38. Sai dogarai suka shaida wa alƙalan wannan magana. Su kuwa da suka ji Bulus da Sila Romawa ne suka tsorata.

Karanta cikakken babi A.m. 16