Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 16:21-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Suna kuma koyar da al'adun da bai halatta mu karɓa ko mu bi ba, da yake mu Romawa ne.”

22. Sai jama'a suka ɗungumo musu gaba ɗaya, alƙalan kuma suka yi kaca-kaca da tufafinsu, suka tuttuɓe su, suka yi umarni a bulale su da tsumagu.

23. Da aka bulale su da gaske, aka jefa su kurkuku, aka umarci yari ya tsare su da kyau.

24. Shi kuwa da ya karɓi wannan umarni, sai ya jefa su can ciki cikin kurkuku, ya sa su a turu.

25. A wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu'a suna waƙoƙin yabon Allah, 'yan sarka kuwa suna sauraronsu,

26. farat ɗaya, sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, har harsashin ginin kurkuku ya raurawa. Nan da nan ƙofofin suka bubbuɗe, marin kowa kuma ya ɓalle.

27. Da yāri ya farka daga barci ya ga ƙofofin kurkuku a buɗe, ya zaro takobinsa, yana shirin kashe kansa, cewa yake 'yan sarƙa sun gudu.

28. Amma Bulus ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Kada ka cuci kanka, ai duk muna nan!”

29. Sai yari ya ce a kawo fitilu, ya yi wuf ya ruga ciki, ya fāɗi gaban Bulus da Sila, yana rawar jiki don tsoro.

30. Sa'an nan ya fito da su waje, ya ce, “Ya shugabanni, me zan yi in sami ceto?”

31. Su kuwa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”

Karanta cikakken babi A.m. 16