Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 15:30-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Su kuma da aka sallame su, suka tafi Antakiya, da suka tara jama'ar, suka ba da wasiƙar.

31. Da suka karanta ta, suka yi farin ciki saboda gargaɗin.

32. Yahuza da Sila kuma, da yake su annabawa ne, suka gargaɗi 'yan'uwa da maganganu masu yawa, suka kuma ƙarfafa su.

33. Bayan sun yi 'yan kwanaki a wurin, sai 'yan'uwa su sallame su lafiya, suka koma wurin waɗanda suka aiko su.

34. [Amma Sila ya ga ya kyautu shi ya zauna a nan.]

35. Bulus da Barnaba kuwa suka dakata a Antakiya, suna koyarwa suna kuma yin bisharar Maganar Ubangiji, tare da waɗansu ma da yawa.

36. An jima, Bulus ya ce wa Barnaba, “Bari yanzu mu koma mu dubo 'yan'uwa a kowane gari da muka sanar da Maganar Ubangiji, mu ga yadda suke.”

37. Barnaba kuwa ya so su tafi da Yahaya, wanda ake kira Markus.

38. Amma Bulus bai ga ya kyautu su tafi da wanda ya rabu da su a ƙasar Bamfiliya, ya ƙi tafiya aiki tare da su ba.

39. Sai matsanancin saɓanin ra'ayi ya auku, har ya kai su ga rabuwa. Barnaba ya ɗauki Markus, suka shiga jirgin ruwa zuwa tsibirin Kubrus,

40. amma Bulus ya zaɓi Sila, bayan 'yan'uwa sun yi masa addu'a alherin Allah ya kiyaye shi, ya tafi.

41. Bulus ya zazzaga ƙasar Suriya da ta Kilikiya, yana ta ƙarfafa Ikilisiyoyi.

Karanta cikakken babi A.m. 15