Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 14:23-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Bayan kuma sun zaɓar musu dattawa a kowace Ikkilisiya, game da addu'a da azumi, suka danƙa su ga Ubangiji, wanda dā ma suka gaskata da shi.

24. Da suka zazzaga ƙasar Bisidiya, suka isa ƙasar Bamfiliya.

25. Da kuma suka faɗi Maganar a Bariyata, suka tafi Ataliya.

26. Daga nan kuma suka shiga jirgin ruwa sai Antakiya, inda tun dā aka yi musu addu'a alherin Allah ya kiyaye su cikin aikin nan da yanzu suka gama.

27. Da suka iso, suka tara jama'ar Ikkilisiya suka ba da labarin dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu, da kuma yadda ya buɗe wa al'ummai ƙofar bangaskiya.

28. Sun kuwa jima a can tare da masu bi.

Karanta cikakken babi A.m. 14