Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Bitrus Ya Yi wa Ikkilisiyar Urushalima Bayani

1. To, manzanni da 'yan'uwan da suke a ƙasar Yahudiya suka ji, cewa al'ummai ma sun yi na'am da Maganar Allah.

2. Da Bitrus ya zo Urushalima, 'yan ɗariƙar masu kaciyar nan suka yi masa sūka,

3. suka ce, “Ga shi, ka shiga wurin marasa kaciya, har ka ci abinci tare da su!”

4. Sai Bitrus ya fara, yana yi musu bayani bi da bi cewa,

5. “Ni dai, ina birnin Yafa ina addu'a, sai wahayi ya zo mini, na ga wani abu na saukowa kamar babban mayafi, an zuro shi daga sama ta kusurwoyinsa huɗu, har ya zo wurina.

6. Da na zuba masa ido, na duba na ga dabbobi, da namomin jeji, da masu jan ciki, da kuma tsuntsaye a ciki.

7. Sai kuma na ji wata murya ta ce mini, ‘Bitrus, ka tashi, ka yanka, ka ci.’

8. Amma na ce, ‘A'a, ya Ubangiji, don ba wani abu marar tsarki ko mai ƙazanta da ya taɓa shiga bakina.’

9. Sai muryar ta amsa daga Sama ta yi magana ta biyu, ta ce, ‘Abin da Allah ya tsarkake, kada ka ce da shi marar tsarki.’

10. An yi wannan sau uku, sa'an nan aka janye abin sama.

11. Ba zato sai ga mutum uku tsaye a ƙofar gidan da muke, an aiko su wurina ne daga Kaisariya.

12. Sai Ruhu ya ce mini in tafi tare da su, ba tare da wata shakka ba. 'Yan'uwan nan shidda kuma suka rako ni, har muka shiga gidan mutumin nan.

13. Sai ya gaya mana yadda ya ga mala'ika tsaye a gidansa, yana cewa, ‘Ka aika Yafa a kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus,

14. shi zai faɗa maka maganar da za ka sami ceto game da ita, kai da jama'ar gidanka duka.’

15. Da fara maganata, Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu, daidai yadda ya sauko mana tun da farko.

16. Sai na tuna da Maganar Ubangiji, yadda ya ce, ‘Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma ku da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.’

17. Tun da yake Allah ya yi musu baiwa daidai da wadda ya yi mana, sa'ad da muka gaskata da Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni in dage wa Allah!”

18. Da suka ji haka, suka rasa ta cewa, suka kuma ɗaukaka Allah suka ce, “Ashe, har al'ummai ma Allah ya ba su tuba zuwa rai.”

Ikkilisiya a Antakiya ta Suriya

19. To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin nan da ya tashi kan sha'anin Istifanas, sun yi tafiya har ƙasar Finikiya, da tsibirin Kubrus, da birnin Antakiya, ba su yin wa'azin Maganar Allah ga kowa sai ga Yahudawa kaɗai.

20. Amma akwai waɗansunsu, mutanen Kubrus da na Kurane a cikinsu waɗanda da isowarsu Antakiya suka yi wa al'ummai magana, suna yi musu bisharar Ubangiji Yesu.

21. Ikon Ubangiji kuwa na tare da su, har mutane da yawa da suka ba da gaskiya suka juyo ga Ubangiji.

22. Sai labarin nan ya kai kunnen Ikkilisiyar da take Urushalima, Ikkilisiyar kuma ta aiki Barnaba can Antakiya.

23. Da ya iso ya kuma ga alherin da Allah ya yi musu, ya yi farin ciki, ya gargaɗe su duka su tsaya ga Ubangiji da dukan zuciyarsu,

24. domin shi mutum ne nagari cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya. Sai mutane masu yawan gaske suka ƙaru ga Ubangiji.

25. Sai Barnaba ya tafi Tarsus neman Shawulu,

26. bayan ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antakiya. Shekara sur suna taruwa da Ikkilisiya, suna koya wa mutane masu yawan gaske. A Antakiya ne aka fara kiran masu bi da suna Kirista.

27. To, a kwanakin nan waɗansu annabawa suka zo Antakiya daga Urushalima.

28. Sai ɗaya daga cikinsu, mai suna Agabas, ya miƙe tsaye, ya yi faɗi da ikon Ruhu, cewa za a yi wata babbar yunwa, a duniya duka, an yi ta kuwa a zamanin Kalaudiyas.

29. Sai masu bi suka ɗaura niyya, kowa gwargwadon ƙarfinsa, su aika wa yan'uwan da suke ƙasar Yahudiya gudunmawa.

30. Haka kuwa suka yi, suka aika wa dattawan Ikkilisiya ta hannun Barnaba da Shawulu.