Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 10:36-48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Allah ya aiko wa Isra'ilawa maganarsa, ana yi musu bisharar salama ta wurin Yesu Almasihu, shi ne kuwa Ubangijin kowa.

37. Kun dai san labarin nan da ya bazu a duk ƙasar Yahudiya, an fara tun daga ƙasar Galili, bayan baftismar da Yahaya ya yi wa'azi,

38. wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.

39. Mu kuwa shaidu ne ga duk abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da Urushalima. Shi ne kuma suka kashe ta wurin kafa shi a jikin gungume.

40. Shi ne Allah ya tasa a rana ta uku, ya kuma yarda ya bayyana,

41. ba ga dukan jama'a ba, sai dai ga shaidun nan da Allah ya zaɓa tun dā, wato mu ke nan, da muka ci muka sha tare da shi, bayan ya tashi daga matattu.

42. Ya kuma umarce mu mu yi wa mutane wa'azi, mu kuma tabbatar cewa shi ne wanda Allah ya sa mai hukunta rayayyu da matattu.

43. Shi ne duk annabawa suka yi wa shaida, cewa albarkacin sunansa duk mai gaskatawa da shi zai sami gafarar zunubai.”

44. Bitrus na a cikin wannan magana, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko wa dukan masu jinta.

45. Sai Yahudawa masu bi, ɗaukacin waɗanda suka zo tare da Bitrus, suka yi mamakin ganin har al'ummai ma an zubo musu baiwar Ruhu Mai Tsarki.

46. Domin sun ji suna magana da waɗansu harsuna, suna ta ɗaukaka Allah. Sa'an nan Bitrus ya ce,

47. “Akwai mai iya hana ruwan da za a yi wa mutanen nan baftisma, waɗanda suka sami Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda mu ma muka samu?”

48. Sai ya yi umarni a yi musu baftisma da sunan Yesu Almasihu. Sa'an nan suka roƙe shi ya ƙara 'yan kwanaki a gunsu.

Karanta cikakken babi A.m. 10