Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 10:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. An yi wani mutum a Kaisariya, mai suna Karniliyas, wani jarumi ne na ƙungiyar soja da ake kira Ƙungiyar Italiya.

2. Shi kuwa mutum ne mai ibada, yana tsoron Allah shi da iyalinsa duka, yana yana ba jama'a sadaka hanu sake, yana kuma addu'a ga Allah a kai a kai.

3. Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma, ya ga wani mala'ikan Allah a fili cikin wahayi, ya shigo, ya ce masa, “Ya Karniliyas.”

4. Shi kuwa ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, mene ne?” Mala'ikan kuma ya ce masa, “Addu'arka da sadakarka sun kai har a gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.

5. To, yanzu, sai ka aiki mutane Yafa su kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus,

6. ya sauka a gun Saminu majemi, wanda gidansa yake a bakin bahar.”

7. Da mala'ikan da ya yi masa magana ya tafi, ya kira barorinsa biyu, da kuma wani soja mai ibada daga cikin waɗanda suke yi masa hidima kullum.

8. Da ya ba su labarin kome, ya aike su Yafa.

Karanta cikakken babi A.m. 10