Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

A.m. 10:1-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. An yi wani mutum a Kaisariya, mai suna Karniliyas, wani jarumi ne na ƙungiyar soja da ake kira Ƙungiyar Italiya.

2. Shi kuwa mutum ne mai ibada, yana tsoron Allah shi da iyalinsa duka, yana yana ba jama'a sadaka hanu sake, yana kuma addu'a ga Allah a kai a kai.

3. Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma, ya ga wani mala'ikan Allah a fili cikin wahayi, ya shigo, ya ce masa, “Ya Karniliyas.”

4. Shi kuwa ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, mene ne?” Mala'ikan kuma ya ce masa, “Addu'arka da sadakarka sun kai har a gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.

5. To, yanzu, sai ka aiki mutane Yafa su kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus,

6. ya sauka a gun Saminu majemi, wanda gidansa yake a bakin bahar.”

7. Da mala'ikan da ya yi masa magana ya tafi, ya kira barorinsa biyu, da kuma wani soja mai ibada daga cikin waɗanda suke yi masa hidima kullum.

8. Da ya ba su labarin kome, ya aike su Yafa.

9. Kashegari suna cikin tafiya, sun zo kusa da gari ke nan, sai Bitrus ya hau kan soro yin addu'a, wajen rana tsaka.

10. Yunwa ta kama shi, har ya so ya ci wani abu. Ana cikin shirya abincin, sai wahayi ya zo masa,

11. ya ga sama ta dare, wani abu kuma yana saukowa kamar babban mayafi, ana zuro shi ƙasa ta kusurwoyinsa huɗu.

12. Cikinsa akwai kowace irin dabba, da masu jan ciki, da tsuntsaye.

13. Sai ya ji wata murya ta ce masa, “Bitrus, tashi, ka yanka ka ci.”

14. Amma Bitrus ya ce, “A'a, ya Ubangiji, don ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko mai ƙazanta ba.”

15. Sai ya sāke jin murya, ji na biyu, ta ce, “Abin da Allah ya tsarkake, kada ka ce da shi marar tsarki.”

16. Da an yi wannan sau uku, nan da nan aka yi sama da abin.

17. Bitrus na a cikin damuwa ƙwarai a kan ko mece ce ma'anar wahayin da aka yi masa, sai ga mutanen da Karniliyas ya aiko tsaye a ƙofar zaure, sun riga sun tambayi gidan Saminu,

18. suna sallama, suna tambaya ko Saminu da ake kira Bitrus a nan ya sauka.

19. Tun Bitrus yana bibiya wahayin nan, Ruhu ya ce masa, “Ga mutum uku nan suna nemanka.

Karanta cikakken babi A.m. 10