Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 6:17-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Ku kuma ɗauki kwalkwalin ceto, da takobin Ruhu, wato Maganar Allah,

18. a koyaushe kuna addu'a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu'a.

19. Ni ma ku yi mini, domin in sami baiwar yin hurci, in yi magana gabagaɗi, in sanar da asirin bishara,

20. wadda ni jakadanta ne, ɗaurarre. Ku dai yi mini addu'a, duk sa'ad da nake yin bisharar, in bayyana ta gabagaɗi, kamar yadda ya kamata in yi.

21. A yanzu kuwa, don ku ma ku san lafiyata, da kuma halin da nake a ciki, ga Tikikus, ƙaunataccen ɗan'uwa, amintaccen mai hidimar Ubangiji, zai sanar da ku kome.

22. Na aiko shi gare ku musamman domin ku san yadda muke, ya kuma ƙarfafa muku zuciya.

23. Salamar Allah Uba da ta Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata ga 'yan'uwa, tare da ƙauna game da bangaskiya.

24. Alheri yă tabbata ga dukkan masu ƙaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu da ƙauna marar ƙarewa.

Karanta cikakken babi Afi 6