Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 6:13-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Saboda haka, sai ku ɗauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa a muguwar ranar nan, bayan kuma kun gama kome duka, ku dage.

14. Saboda haka fa ku dage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama sulkenku,

15. shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a ƙafafunku.

16. Banda waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kiban wutar Mugun nan da ita.

17. Ku kuma ɗauki kwalkwalin ceto, da takobin Ruhu, wato Maganar Allah,

18. a koyaushe kuna addu'a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu'a.

19. Ni ma ku yi mini, domin in sami baiwar yin hurci, in yi magana gabagaɗi, in sanar da asirin bishara,

20. wadda ni jakadanta ne, ɗaurarre. Ku dai yi mini addu'a, duk sa'ad da nake yin bisharar, in bayyana ta gabagaɗi, kamar yadda ya kamata in yi.

21. A yanzu kuwa, don ku ma ku san lafiyata, da kuma halin da nake a ciki, ga Tikikus, ƙaunataccen ɗan'uwa, amintaccen mai hidimar Ubangiji, zai sanar da ku kome.

22. Na aiko shi gare ku musamman domin ku san yadda muke, ya kuma ƙarfafa muku zuciya.

Karanta cikakken babi Afi 6