Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Afi 6:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku 'ya'ya, ku yi wa iyayenku biyayya tsakani da Ubangiji, domin wannan shi ne daidai.

2. Wannan shi ne umarnin farko mai alkawari, cewa, “ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,

3. don al'amarinka ya kyautatu, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”

4. Ku ubanni, kada ku sa 'ya'yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da tarbiyya, da kuma gargaɗi ta hanyar Ubangiji.

5. Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya, da hali bangirma tare da matsananciyar kula da zuciya ɗaya, Almasihu kuke yi wa ke nan,

6. ba aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai kamar bayin Almasihu masu aikata abin da Allah yake so, da zuciya ɗaya,

7. kuna bauta da kyakkyawar niyya domin Ubangiji kuke yi wa, ba mutane ba.

8. Kun sani, kowane alherin da mutum ya yi, ko shi ɗa ne ko bawa, Ubangiji zai sāka masa shi.

9. Ku iyayengiji, ku ma ku yi musu haka, ku bar tsorata su, ku sani, shi wanda yake Ubangijinsu da ku duka, yana Sama, shi kuwa ba ya zaɓe.

10. A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.

Karanta cikakken babi Afi 6